Matthew 27

Yahuda Ya Rataye Kansa

1Da wayewar gari, sai dukan manyan firistoci da dattawan mutane suka yanke shawara su kashe Yesu. 2Suka ɗaure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga gwamna Bilatus.

3Saʼad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin. 4Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.”

Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.”

5Sai Yahuda ya zubar da kuɗin a cikin haikalin ya tafi. Saʼan nan ya je ya rataye kansa.

6Manyan firistoci suka ɗauki kuɗin, suka ce, “Doka ta hana a sa kuɗin a cikin maʼaji, da yake kuɗin jini ne.” 7Saboda haka, sai suka yanke shawara su yi amfani da kuɗin suka sayi filin mai yin tukwane, saboda binne baƙi. 8Shi ya sa ake kiran filin, Filin Jini har yǎ zuwa yau. 9Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa, “Suka ɗauki azurfa talatin, kuɗin da mutanen Israʼila suka sa a kansa, 10suka kuma yi amfani da su, suka sayi filin mai yin tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”
Dubi Zak 11.12, 13; Irm 19.1-13; Irm 32.6-9


Yesu A gaban Bilatus

11Ana cikin haka, Yesu kuwa yana tsaye a gaban gwamna, sai gwamnan ya tambaye shi, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce, “I, haka ne, kamar yadda ka faɗa.”

12Da manyan firistoci da dattawa suka zarge shi, bai ba da amsa ba. 13Sai Bilatus ya tambaye shi, ya ce, “Ba ka jin shaidar da suke kawowa a kanka?” 14Amma Yesu bai ce uffan game da ko ɗaya daga cikin zargin da suka yi masa ba. Har gwamna ya yi mamaki ƙwarai.

15A wannan irin Biki, gwamna yana da wata alʼada, ta sakin ɗan kurkuku guda wanda taron suka zaɓa. 16To, a wannan lokaci kuwa suna da wani shahararren ɗan kurkuku da ake kira Barabbas. 17Saboda haka da taron suka taru, sai Bilatus ya tambaye su, ya ce, “Wane ne a cikinsu kuke so in sakar muku: Barabbas ko Yesu wanda ake kira Kiristi?” 18Don ya san saboda kishi ne suka ba da Yesu a gare shi.

19Yayinda Bilatus yake zaune a kan kujerar shariʼa, sai matarsa ta aika masa da wannan saƙo cewa, “Kada ka sa hannunka a kan marar laifin nan, domin na sha wahala ƙwarai, a cikin mafarki yau game da shi.”

20Amma manyan firistoci da dattawa suka shawo kan taron, su ce, a ba su Barabbas, amma a kashe Yesu.

21Gwamna ya yi tambaya, ya ce, “Wane ne cikin biyun nan, kuke so in sakar muku?”

Suka ce, “Barabbas.”

22Bilatus ya yi tambaya, “To, me zan yi da Yesu wanda ake kira Kiristi?”

Duka suka ce, “A gicciye shi!”

23Bilatus ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?”

Amma suka ƙara ta da ihu, suna cewa, “A gicciye shi!”

24Da Bilatus ya ga cewa ba ya kaiwa koʼina, sai ma hargitsi ne yake so yǎ tashi, sai ya ɗibi ruwa, ya wanke hannuwansa a gaban taron, ya ce, “Ni kam, ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan. Wannan ruwanku ne!”

25Sai dukan mutane suka amsa, suka ce, “Bari alhakin jininsa yǎ zauna a kanmu da ʼyaʼyanmu!”

26Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, saʼan nan ya ba da shi a gicciye.

Sojoji Sun Yi wa Yesu Baʼa

27Sai sojojin gwamna suka ɗauki Yesu suka kai shi Fadar mai mulki, saʼan nan suka tara dukan kamfanin sojoji kewaye da shi. 28Suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar riga. 29Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a ka. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa baʼa, suna cewa, “Ranka yǎ daɗe sarkin Yahudawa!” 30Suka tattofa masa miyau, suka karɓe sandan, suka yi ta ƙwala masa shi a kai. 31Bayan sun yi masa baʼa, sai suka tuɓe masa rigar, suka sa masa nasa tufafin. Sai suka tafi da shi, domin su gicciye shi.

Gicciyewa

32Suna fitowa ke nan, sai suka sadu da wani mutumin Sairin, mai suna Siman. Sai suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen. 33Sai suka iso wani wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai). 34A can, suka ba shi ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yǎ sha. Amma da ya ɗanɗana, sai ya ƙi sha. 35Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuriʼa. 36Saʼan nan suka zauna suna tsaronsa. 37Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce, “WANNAN SHI NE YESU SARKIN YAHUDAWA.” 38An gicciye ʼyan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗaya kuma a hagunsa. 39Masu wucewa, suka zazzage shi, suna kaɗa kai, 40suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!”

41Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa baʼa, suna cewa, 42“Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Israʼila! To, yǎ sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi. 43Ya dogara ga Allah. Bari Allah yǎ cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ” 44Haka ma, ʼyan fashin da aka gicciye tare da shi, suka zazzage shi.

Mutuwar Yesu

45Daga saʼa ta shida, har zuwa saʼa ta tara, duhu ya rufe ƙasa duka. 46Wajen saʼa ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi,
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā suna da Eli, Eli ne a nan
lama sabaktani”— wanda yake nufi, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”
Zab 22.1


47Saʼad da waɗanda suke tattsaye a wurin suka ji haka, sai suka ce, “Yana kiran Eliya.”

48Nan da nan, ɗaya daga cikinsu ya ruga, ya sami soso, ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya sa a sanda, ya miƙa wa Yesu, yǎ sha. 49Sauran kuwa suka ce, “Ƙyalle shi mu ga, ko Eliya zai zo yǎ cece shi.”

50Da Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sai ya saki ruhunsa.

51A daidai wannan lokaci, sai labulen haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta jijjiga, duwatsu kuma suka farfashe. 52Kaburbura suka bubbuɗe, jikunan tsarkaka da yawa kuwa cikin waɗanda da suka mutu, suka tashi.

53Suka firfito daga kaburbura, saʼan nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa.

54Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizan ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!”

55Akwai mata da yawa a can, suna ƙallo daga nesa. Sun bi Yesu tun daga Galili, suna masa hidima. 56A cikinsu, akwai Maryamu Magdalin, da Maryamu uwar Yaƙub da Yoses, da kuma uwar ʼyaʼyan Zebedi.

Bizinar Yesu

57Da yamma ta yi, sai ga wani mutum mai arziki daga Arimateya, sunansa Yusuf, wanda shi da kansa almajirin Yesu ne. 58Ya je wurin Bilatus, ya roƙe shi yǎ ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a ba shi. 59Yusuf ya ɗauki jikin ya nannaɗe shi da zanen lilin mai tsabta. 60Saʼan nan ya sa shi a sabon kabarinsa, wanda ya haƙa a dutse. Bayan ya gungura wani babban dutse ya rufe bakin kabarin, sai ya tafi abinsa. 61Maryamu Magdalin da ɗayan Maryamun, suna zaune a wurin, ɗaura da kabarin.

Masu Gadi a Kabari

62Washegari, wato, bayan Ranar Shirye-shirye, sai manya firistoci da Farisiyawa, suka je wurin Bilatus. 63Suka ce, “Ranka yǎ daɗe, mun tuna, mai ruɗin nan tun yana da rai, ya ce, ‘Bayan kwana uku, zan tashi daga matattu.’ 64Saboda haka, ka ba da umarni, a tsare kabarin sai rana ta uku ɗin. In ba haka ba, almajiransa za su iya zuwa su sace jikin, saʼan nan su faɗa wa mutane cewa, an tashe shi daga matattu. Ruɗin ƙarshen nan fa, sai yǎ fi na farkon muni.”

65Sai Bilatus ya ce, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare kabarin iya ƙoƙarinku.” 66Sai suka je suka tsare kabarin ta wurin buga masa hatimi, suka kuma sa masu gadi.

Copyright information for HauSRK